Rundunar yan sandan Jihar Ribas ta tabbatar da kama wata mata mai shekaru 39 bisa zargin laifin siyar da jarirai.

Kwamishinan yan sandan jihar Polycarp Emeka shi ne ya bayyana haka ga yan Jaridu.

Ya ce sun samu nasarar kama matar a gidanta bayan ta tara mata suna haihuwa kuma ta na siyar da jariran wanda hakan sabawa doka ne.

Sannan sun kubutar da mata akalla shida daga gidan wadda ake zargin wadda kuma ta amsa laifinta.
Wannan matasalar dai ta siyar da yara ba yanzu aka fara ba a kasa Najeriya musamman ma a kudanci, inda ake yawan samun matasalar dukda hukumomi na iya kokararin su.
A wasu lokatan ma akan dibi yara kanan sai a siyar da su zuwa wasu kasashen waje ko ma a chanza musu addinin iyayensu wanda doka ta hana.