Sabon Shugaban Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Kasa NAHCON a Jihar Kano Rabi’u Danbappa ya zargin tsohon shugaban hukumar da aikata damfarar maniyyata aikin hajji bana suka biya kudaden kujeru 190 wanda su ka kasance na bogi.

Sabon shugaban Wanda ya karbi ragamar hukumar a yammacin ranar Alhamis, ya bayyana cewa ya tarar an sayar da kujeru fiye da wadanda Hukumar Aikin Hajji a Kasa (NAHCON) ta bai’wa jihar.

Dan Bappa ya kara da cewa a ka’ida Hukumar NAHCON ta bai’wa Jihar Kano kujeru 6,082, inda kuma shugaban hukumar ya sayar da kujeru 6,273.

Shugaban ya ce tsohon shugaban ya nemi karin kujeru daga Hukumar NAHCON inda ta shaida masa cewa ba ta da wasu kujeru da za ta iya kara wa Jihar ta Kano.

Sabon shugaban ya bayyana cewa bayan da su ka tuntubi Shugaban Hukumar NAHCON Alhaji Zikirullah Kunle Hassan ya bayyana musu cewar basu da kujerun da za su iya karawa hukumar ta Kano,inda ya ce su nemi tsohon shugaban Hukumar domin neman kudaden sauran kujerun mutanen da ya karba.

Sannan ya ce hakan ba daidai ba ne sayar da abinda baka dashi a hannu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: