Kungiyar kwadago a Najeriya sun yi watsi d abatun cire tallafin man fetur da shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi.

Kungiyar ta shirya tsunduma yajin aiki a ranar Laraba mako mai zuwa.
Hakan na zuwa ne bayan furucin shugaba Bola Ahmed Tinubu da yayi a ranar rantsar da shi na dakatar da bayar da tallafin man fetur.

Shugaban ƙungiyar kwadago na kasa Joe Ajaero ya ce za su tsunduma yajin aikin gama gari na ƙasa baki daya a ranar Laraba.

Umarnin hakan na zuwa ne bayan da su ka yi wani taron gaggawa a Abuja.
Shugaaban ya ce muddin gwamnati ba tayi wani abu a kai baza ta haifar da zanga-zanga a kasar baki daya.