Hukumar kashe gobara reshen Jihar Kano ta tabbatar da mutuwar wani almajiri mai shekara 13 bayan ya fada cikin wani ruwa a kauyen Makugara da ke Karamar Hukumar Karaye a Kano.

 

Mai magana da yawun hukumar Saminu Yusuf Abdullahi ne ya tabbatar da hakan a ranar Juma’a, inda ya ce almajirin mai suna Yusuf Magaji ya rasa ran nasa ne a lokacin da shi da wasu sauran abokansa almajirai suke wanki a bakin rafin.

 

Ya ce almajiran su na tsaka da wanda santsi ya kwashi ɗaya a ciki qanda yakan ya sa ya faɗa cikin ruwan.

 

Ya ce sun smau kiran gaggawa daga maalamain makarantar kuma kafin su je mutaane sun yi nasarar dakkoshi.

 

Sai dai baayan kai shi asibiti likita ya tabbatar daa mutuwarsa.

 

Saminu Yusuf ya bayyana cewa mutanen gurin sun yi nasarar ceto almajirin a mawuyacin hali inda suka garzaya da shi zuwa Asibitin garin na Karaye likitoci suka tabbatar da mutuwar almajirin.

 

Saminu Abdullahi ya ce sun mika gawar mamacin ga Malam Nafi’u Na Adama domin yi masa sutura.

 

Kakakin ya bayyana cewa almajirin da sauran abokansa sun fita ne daga Makarantar Malam Nafiu Na Adama da ke Karamar hukumar ta Karaye.

 

Saminu ya ce yaran suna tsaka da wanka a gefen rafin ne santsi ya kwashi almajirin ya fada a ciki.

 

Kakakin ya kara da cewa Malamin tsangayar ne ya yi wa hukumar kiran gaggawa ya sanar da ita cewa almajirinsa ya fada a cikin rafin.

 

Kazalika Saminu ya ce almajiran suna kan hanyarsu ta komawa kauyen ne suka tsaya domin yin wanka a gefen rafin inda aka yi rashin sa’a daya daga cikinsu ya fada a ciki.

 

Saminu Yusuf ya bayyana cewa mutanen gurin sun yi nasarar ceto almajirin a mawuyacin hali inda suka garzaya da shi zuwa Asibitin garin na Karaye likitoci suka tabbatar da mutuwar almajirin.

 

Saminu Abdullahi ya ce sun mika gawar mamacin ga Malam Nafi’u Na Adama domin yi masa sutura.

 

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: