Rundunar Sojin Najeriya sun samu nasarar hallaka mayakan kungiyar Boko Haram da ISWAP guda 80 a yayin da wasu 876 suka mika wuya a makonni biyun da suka gabata.

Mai magana da yawun rundunar Manjo-Janar Musa Danmadami ne ya tabbatar da hakan ya ce sojojin hadin gwiwa da ke Tafkin Chadi MNJTF sun hallaka kwamandoji da mayakan kungiyar ISWAP 55 a yankin Arege da ke Karamar Hukumar Abadam ta Jihar Borno.


Jami’an Sojoji sun kuma kashe mayakan Boko Haram da ISWAP 25 tare da kwato bindigogi 30 da kunshin harsashin bindiga kirar AK-47 guda 12 da gurneti daya da sauran makaman su.
Daga cikin mayakan akwai iyalansu wadanda suka hada da maza 89 da mata 249 da kananan yara 538 sun mika wuya ga sosoji da sauran jami’an a gurare daban-daban da ke Jihar.
Kwararre akan sha’anin tsaro a yankin Tafkin Kasar Chadi Zagazola Makama ya bayyana cewa jami’an sun lalata motoci 13 da babura da na’urorin tayar da abubuwan fashewa guda biyar mallakin ‘yan ta’addan.
Janar Danmadami ya kara da cewa an kashe kwamandojin kungiyar da dama a wani samame na kwanaki 22 wanda ya kare a ranar 28 ga Mayu, 2023 a yankin Harbin Zuma da ke Gabar Tafkin Chadi.
Dan Madami ya kara da cewa daga ranar 18 ga watan Mayu zuwa 1 ga Yuni sojoji suka kai wani samamen domin fatattakar ’yan mayakan daga sansanoninsu da aka gano a wasu kauyuka da dazuzzuka da tsaunukan Konduga da Abadam.
Sauran sun hada da Guzamala da Ngala da Bama da Dikwa da Gubio da Damboa da Jere da Kukawa da kuma Magumeri duk da ke Jihar.
A yayin taron wani taron karawa juna sani kan ayyukan jami’an sojoji tare da nasarorin da suka samu wanda rundunar ta shirya a hedikwatarta da ke Maiduguri ya ce nasara ta samu ne a kokarin jami’an sojoji na kawo karshen ’yan ta’adda da sauran masu aikata miyagun laifuka a yankin Arewa maso Gabashin Najeriya.