Wasu ‘yan bindiga sun kai wani hari ƙauyen Ketti da ke yankin ƙaramar hukumar Abuja Municipal AMAC tare da yin Garkuwa da basaraken Kauyen Mista Sunday Zakwoyi.

 

 

 

‘Yan bindigan bayan sun yi garkuwa da Basaraken suka hada da wani dan gidan Sarauta Mista Markus Gade da wani mazauni ɗaya.

 

 

 

Mazauna Kauyen sun bayyana cewa ‘yan bindigan akalla su Goma sun shiga garin ne Dauke da manyan bindigu da misalin ƙarfe 11:30 na daren ranar Alhamis.

 

 

 

Mazauna kauyen sun kara da cewa ‘yan bindigan sun fara aikata ta’addancin su ne tun daga wannan lokaci har ƙarfe 12:50 na farkon daren ranar Jumu’a inda su ka dinga harbin mazauna kauyen.

 

 

 

Hakimin Ketti Mista Alex Akata ya tabbatar da faruwar lamarin tare da yin kira ga hukumomin tsaro su kai musu dauki sakamakon barazanar da su ke yi musu.

 

 

 

Hakimin ya ce makwanni uku da suka gabata masu garkuwar su ka yi garkuwa da mutanen garin akalla su Uku ciki har da wani Danladi Aliyu wanda har yanzu yana hannunsu.

 

 

 

Sannan Basaraken ya koka kan cewa rashin kayan aiki ne babban abinda ke kara kawo tabarbarewar tsaro a yankinsu, daga bisani ya bukaci shugaban ƙaramar hukumar AMAC da mahukuntan Abuja su dube su.

 

 

 

Hakimin ya ce duk tsawom lokacin da maharan suka shafe suna aikata ta’adi a garin, babu jami’in tsaron da ya kawo musu ɗauki.

 

 

 

Wani dan uwan daya daga cikin mutanen da aka yi garkuwa da su ya ce sun turawa ‘yan bindigar kuɗin fansa amma har kawo yanzu basu sako su ba.

 

 

 

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: