Ƙungiyar ma’aikatan kotuna a Najeriya JESUN ta amince wajen marawa kungiyar ƙawadago NLC baya wajen tsunduma yajin aiki a ranar Laraba mai zuwa.

Idan ba a manta ba, ƙungiyar ƴan jarida da ƙungiyar ma’aikatan wutan lantarki a Najeeriya sun shirya tsuduma yajin aikin sanadin janye tallafin man fetur a Najeriya.

Ƙungiyar ƙwadago ta shirya tafiya yajin aiki ranar Laraba sakamakon cire tallafin man fetur har ma ƙungiyar ta yi barazanar yin zanga-zanga a kasar muddin ba a dawo da tallafin ba.

Ko a jiya Lahadi ƙungiyar ta zauna da ɓangaren gwamnatin tarayya a kai, sai dai ba a cimma matsaya a dangane da lamarin ba.

Mataimakin sakataren ƙungiyar ma’aikatan kotuna a Najeriya Barista Sa’idu Magaji ya shaidawa BBC cewar sun karɓi wasiƙa daga ƙungiyar ƙwadago kuma za su mara musu baya a ranar Laraba.

Y ace za su rufe dukka kotuna, kamar yadda ƙungiyar ta buƙata.

Ƙungiyar ƙwadago ta NLC na cigaba da aike da wasiƙa rassan ƙungiyoyi a Najeriya domin ganin an tafi yajin aikin baki ɗaya.

Matakin ya biyo bayan furucin shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu na cire tallafin man fetur wanda y ace gwamnatin za ta yi haka ne domin saƙon ya dinga zuwa wajen talaka kai tsaye ta hanyar karkatar da kuɗaɗen zuwa ayyukan da talaa zai amfana.

Leave a Reply

%d bloggers like this: