Kamfanin mai a Najeriya NNPCL y ace wa’adin kwantiragin musyar ɗanyen mai da ya saba yi ya zo ƙarshe.

 

Shugaban kamfanin Malam Mele Kyari ne ya bayyana haka yayin ganawarsa da gidan jaridar Reuters ranar Asabar.

 

Ya ce nan ba da jimawa ba kamfanoni masu zaman kansu za su fara siyo man tare da shigo da shi cikin ƙasar ba da daɗewa ba.

 

Ya ce hakan na daga cikin shirin shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu.

 

Kamfanin na musayar danyen mai tare da karbar tatacce daga kasuwar duniya tun a shekarar 2026 sanadin rashin kudin da za aiya siyo man.

 

Shugaban y ace wannan ne karo na farko da kamfanin NNPC ya dakatar da musayar danyen man daga manyan yan kasuwar duniya domin shigo da tataccen man fetur.

 

Sai dai a wannan lokaci kamfanin zai dinga amfani da tsabar kudi wajen siyo tataccen man ferur.

 

Ko da yake, farashin man ya tashi a kasuwar duniya bayan da aka rage fitar da danyen mai da wasu kasashen larabawa su ka yi.

 

A Najeriya, ma fetur yay i tashin gwauron zabi tun bayan da shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya fusta cewar bayar da tallafin mai ya zaman tarihi.

 

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: