Gwamnan Jihar Sokoto Ahmad Aliyu yayi wata ganawa da Majalisar tsaron Jihar bayan a kan batun ‘yan bindiga su ka kai wasu hare-hare Kauyukan Jihar.

Gwamnan yayi ganawar ne akan abinda ya shafi tsaro a Jihar tare da yawaitar hare-haren ‘yan ta’adda akan mutanen Jihar.

A yayin ganawar gwamnan yayi alkwarin kawo karshen maharan da su ka addabi al’ummar Jihar ta Sokoto.

Ganawar wadda aka gudanar a yammacin ranar Litinin mai magana da yawun gwamnan Abubakar Bawa ya shaidawa manema labarai cewa sun gudanar da taron ne domin samar da hadin gwaiiwa da sauran jami’an tsaron a JIHAR.

Kazalika gwamnan ya nuna rashiin jindadin sa akan masu kai’wa ‘yan ta’addan bayanan sirri, inda ya ce dole ne a tashi tsaye domin a kawo karshen su a fadin Jihar.

Gwamnan ya kuma yi musu alkawarin biyan su bashin alawus-alawus din da su ke bi na tsawon watanni Biyar wanda Jami’an tsaron Operation hadin kai su ke bin gwamnatin Jihar.

Sannan ya bayyana cewa gwamnatin sa za ta magance matsar da rundunar ke fuskanta domin ci gaba da gudanar da aikin ta yadda ya kamata.

  • Idan ba a mantaba dai ‘Yan bindigan sun kai wasu hare-haren ne a ranar Asabar a kauyuka uku da ke cikin karamar hukumar Tangaza ta Jihar tare da wasu Kauyuka biyu da ke Yankin Gwadabawa, inda su ka hallaka mutane 37 a Harin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: