Gwamnn Jihar Zamfara Dauda Lawal Dare yayi alkawarin tallafawa ‘yan uwan wadanda mahara su ka hallaka a wasu hare-hare da su ka kai kauyukan Sakiddar Magaji Janbako da ke karamar huukumar Maradun ta Jihar.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a yayin wata ziyarar jaje da ya kai’wa Al’ummar Kauyukan da abin ya shafa.

Lawal Dare wanda ya samu wakilcin Mataimakinsa Malam Mani Malam Mumini ya bayyana cewa gwamnatin Jihar za ta tsaya tsayin daka wajen kawo karshen yawaitar hare-haren batagari a Jihar.

Malam Mumini ya kara da cewa gwamnatin Jihar na kokarin ganin ta samar da hanyoyin da ya kamata wajen ganin ta taimakawa marasa karfi da kuma sauran mutanen da su ke fama da matsalar ‘yan ta’adda da masu satar shanu wadanda su ka shafe tsawon shekaru suna cin karansu babu babbaka.

Shi ma a jawabinsa daraktan yada labaran Jihar Malam Nuhu Salihu Anka ya bayyana cewa gwamnatin ta bayar da tallafin naiira Miliyan Biyu ga ‘yan uwan wadanda harin ya rutsa da su, inda ya ce nan bada dadewa ba jami’an tsaro za su fara gudanar da aiki domin kawo karshen ta’addancii a Jihar tare da samar da wani tsari da zai saukawa mutanen wahalar da su ke fama da ita.

Sannan ya ce gwamnatin za ta kara aikewa da karin jami’an tsaro Kauyukan da abin ya shafa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: