Gwamnan jihar Kaduna, Malam Uba Sani, ya zargi wasu tsoffin gwamnoni a Arewa maso Yamma da cin amanar ƙawancen da jihohi suka ƙulla don samar da tsaro.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito Gwamnan na cewa tsoffin gwamnonin sun yi wa ƙawancen zagon ƙasa ta hanyar, ɗasawa, tare da yan bindiga.

Uba Sani, wanda ya ƙi ambatar suna a zarginsa, ya yi ikirarin wasu gwamnoni sun ɗauki, hanyar da ba zata ɓulle ba, wajen shawo kan rashin tsaro a jihohinsu.

A cewarsa, ɗaukar irin waɗannan hanyoyin marasa kyau ne suka jawo arewa ta wayi gari cikin ƙaƙanikayi da tabarbarewar tsaro mai muni.

Gwamna Sani ya faɗi haka ne a wata hira da gidan talabiji na Channels cikin shirin Sunrise Daily ranar Talata.

Gwamnan ya ƙara da cewa ƙirƙirar yan sandan jihohi ne hanya ɗaya tilo da zata iya kawo karshen kalubalen tsaro a Najeriya.

Ya ce wannan ya zama kusan wajibi idan aka yi la’akari da ƙarancin karfin ikon gwamnoni a kan hukumomin tsaro.

Leave a Reply

%d bloggers like this: