Gwamnan Jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya amince da nadin Alhaji Habu Muhammad Fagge a matsayin shugaban gudanarwa na hukumar fansho ta jihar.

Wannan na cikin wata sanarwa da babban sakataren yada labaran gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar a ranar Talata.

Nadin ya fara aiki ne nan take kamar yadda gwamnan ya bayar da umarnin karbar ragamar aikin hukuma cikin sa’o’i 24.

Alhaji Habu Fagge, wanda ya kammala karatunsa a fannin sha’anin Kudi a Jami’ar Abraham Lincoln.

Ya rike mukamai daban-daban a ma’aikatan gwamnatin Jihar Kano da suka hada da daraktan kudi, daraktan tsare-tsare, bincike da kididdiga da darakta a hukumar tara haraji.

Leave a Reply

%d bloggers like this: