Zaɓaɓɓen Sanata da zai wakilci Zamfara ta yamma a majalisar dattawa, Abdulaziz Yari, bai da niyyar hakura da takarar da yake yi a karkashin APC a kan shugabancin a majalisa ta goma.

Jaridar The Cable ta ruwaito Abdulaziz Yari ya na mai cewa Ubangiji Madaukakin Sarki ne kurum zai zabi wanda zai jagoranci majalisar dattawa ba wani ‘Dan Adam ba.
Jam’iyyar APC mai-ci ta zabi tsohon Ministan harkokin Neja-Delta, Sanata Godswill Akpabio a matsayin ‘dan takaranta, amma sam Abdulaziz Yari bai sallama ba.

Da yake magana da kungiyar mutanen Kudu maso kudu da suka kai masa ziyara, zababben Sanatan ya ce a karshe kaddarar Ubangiji (SWT) za tayi aiki.

An ruwaito tsohon Gwamnan na jihar Zamfara ya nuna babu dalilin yin rigima a kan shugabancin majalisar tarayyar, yake cewa a bar wa Ubangiji ikonsa.