Kwamitin harkokin jiragen sama na majalisar wakilan tarayya, ya bukaci gwamnatin Najeriya ta dakatar da shirin kafa kamfanin Nigeria Air.

Jaridar Premium Times ta ce shugaban kwamitin, Nnolim Nnaji, ya karanto matsayar da suka dauka bayan sun yi wani zama a kai a ranar Talata.
Zaman da aka yi ya samu halartar ‘yan kungiyar AON ta masu jiragen sama da wakilan ma’aikatar tarayya da sauran masu ruwa da
tsaki a kasar.

Sakataren din-din-din na ma’aikatar harkokin jiragen sama, Emmanuel Meribole ya nuna cewa shigo da jirgin da aka yi ba ya nufin kaddamar da kamfanin.

Emmanuel Meribole yake cewa hakan ya nuna niyyar gwamnatin tarayya ne, ya ce tun farko Nigeria Air bai samu lasisin fara aiki daga hannun AOC ba.
Olumide ya ce jirgin da ya sauka a babban filin tashin jirage na Nnamdi Azikiwe a Abuja ba nasu ba ne, ya kara da cewa duk bai san abin da ake ciki a kai ba.
Da ake tattaunawa kan batun a majalisar dattawa, shugaban kwamitin jiragen sama, Sanata Biodun Olujimi ta ce akwai alamar tambaya kan Nigeria Air.
A rahoton jaridar Punch, an ji majalisar wakilan tarayya ta ce ba ta adawa da kafa kamfani na kasa, amma kwamitin jiragen ya ce dole ne ayi komai cikin gaskiyavda tsari.
Matsayar da aka dauka sun hada da dakatar da aikin nan-take, shugaba Bola Tinbu ya kafa kwamiti don sake bincike, sannan a hukunta wadanda aka samu da laifi.