Yayin da ake shirin rantsar da zababbun ‘yan majalisar wakilan tarayya da na dokoki, masu neman shugabanci sun yi nisa a shirye-shiryensu.

Ganin an kammala tattaunawa da ‘yan kwadago a kan batun cire tallafin man fetur, jaridar The Nation ta ce hankalin shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma kan ‘yan majalisa.
Ana sa ran ba da dadewa ba, Mai girma Bola Ahmed Tinubu ya yi maganar shirin rantsar da sababbin Sanatoci da ‘yan majalisar wakilai a makon gobe.

Jaridar ta ce a yau ne Shugaba Tinubu zai ya hadu da gwamnonin jihohin APC mai-mulki da kuma shugabannin jam’iyyar (NWC) kan batun zaben majalisar.

Bayan wannan taro da za ayi, a gobe Tinubu zai hadu da zababbun Sanatoci na jamiyyar APC.
Kafin nan, shugaban ya yi zama na musamman da zababbun ‘yan majalisar wakilan tarayya na APC da nufin kai ya hadu wajen zaben shugabanninsu.
Haka zalika sabon shugaban na Najeriya ya sa labule da ‘yan majalisar da ke adawa da Tajudeen Abbas, su ka dage a kan cewa sai sun tsaya takara da za ayi.