Akalla gidaje 20 ake zargin sun rushe tare da mutuwar mutane biyu bayan wata guguwar iska mai karfin gaske da aka yi a jihar Jigawa.

 

Shugaban karamar hukumar Ringim shehu Udi shi ne ya bayyana haka lokacin tattaunawa da yan Jaridu a ofishinsa dake karamar hukumar ta Ringim jiya Laraba.

 

Ya ce akalla mutane biyu ne suka mutu da kuma gidaje 20 da suka rushe lokacin wata iska ta taso a yankin.

 

Inda lamarin ya faru sun hada da Larabawa da Hambarawa a karamar hukumar Ringim a ranar Litinin cikin dare.

 

Wadanda hadarin ya shafa sun tattauna da kamfanin dillacin labarai na kasa wato NAN.

 

Wani da lamarin ya shafa mai suna Aminu Hadi ya bayyana cewa ya rasa gidansa a lokacin Iskar ta taso.

 

Sannan ya ce yana mai rokon masu hannu da shuni da kungiyoyi masu zaman kansu hadi da gwamnatin jihar da ta taimaka ta duba halin da suke ciki.

 

Sannan kamar yadda suka fada karamar hukumar ta je don taimakansu a bayanin da jaridar Daily Najeriya ta samu.

 

 

 

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: