Wata kotun shari’ar musulunci ta aike da wani mai sana’ar kidan DJ zuwa gidan gyaran hali a jihar Kano.

 

Alkalin kotun mai Shari’a Malam Munzali Idiris Gwadabe shi ne ya aike da matashin zuwa gidan gyaran halin.

 

Tun farko dai ana tuhumar matashin da takurawa wasu masu karatun islamiyya bayan ya kunna kidan.

 

Sai dai yace shima ansakuwwar masu karatun tana takura masa dalilin da ya sa ya nemi ya danne tasu ansakuwwar.

 

Sai dai bayan karanto laifin da aka yi sai ya amsa laifinsa babu bata lokaci.

 

Mai Shari’ar ya aike da shi izuwa gidan yari don gyara halinsa akan saba doka a jiya Laraba.

 

Matsalar kidan DJ dai ta zagaye wurare da yawa musamman lokutan bukukuwa

 

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: