Akalla wasu mutasa biyu ake zargin sun rasa rayukansu a lokacin da ake rusau a masallacin Idi dake kwaryar birni kanon Dabo.

Wani shaida ya bayyana cewa daya daga cikin matashin da ya rasa ransa ya dakko kofofi ne tare da wasu kayan karafuna inda mota take gudanar da rusau.


Sannan motar ta tureshi ya mutu nan take a gurin.
Sai kuma wani shi ma da ake zargin ya rasu bayan gini ya fado musu suna dibar kayan dake cikin shagunan da aka rushe wasu kuma suka samu rauni kamar yadda Daily trust ta rawaito.
Lamarin rusau da gwamnatin jihar Kano ta dakko tun bayan rantsar da gwamnatin jihar ta Abba Abba Kabir Yusuf wanda ya dade da cin alwashi ya jawo ce-ce-ku ce inda a gefe guda Kuma aka samu wasu da yawa galibinsu matasa ne ke dibar kayan wuraren da aka rushe a matsayin ganima.
Amma fa malamai na cewa babu inda hakan ya zama ganima tun da kayan mutane ne ake diba don haka ba halak ba ne kamar yadda Farfesa Umar Sani Fagge ya shaida.
Kuma suma rundunar yan sandan jihar Kano na ci gaba da neman wadanda ke diban kayan mutane suna ayyana shi da cewa ganima.