Wata Gobara ta tashi a kasuwar Damaturu babban birnin jihar Yobe.

Gobarar ta tashi ne da misalin ƙarfe 1:00 na dare ranar Juma’a inda ba a samu nasarar kashe wutar ba sai misalin karfe 4:00 na safiyar yau Asabar.


Jaridar Punch ta ruwaito cewa a yayin tashin gobarar ‘yan Kasuwar sun tafka asara kayayyaki da dama.
Wani mazaunin Jihar mai suna Babannan Garba ya bayyana cewa kayayyaki na miliyoyin naira ne suka lalace sanadiyyar tashin gobarar.
Bayan tashin wutar gwamnatin Jihar ta ce za ta bai’wa ‘yan Kasuwar tallafi a lokacin gwamnan Jihar ya aike da saƙon jaje kan waɗanda gobarar ta ritsa da su.
A cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun hadimin gwamnan Mamman Mohammed ya ce gwammnatin za ta kawowa ‘yan Kasuwar agaji ne domin rage musu radadin halin da su ke ciki.
Sanarwar ta kara da cewa nan bada jimawa ba za a bai’wa ƴan kasuwar sabbin kasuwannin zamani na Damaturu da Gashua da Nguru domin komawa cikin muhalli wanda ya ke da tsaro sosai, domin kare su daga iftila’in yawaitar tashin gobara a kasuwanni.
Mamman ya kara da cewa sabbin kasuwannin da aka ginasu an gina ne da fasahar magance matsalar tashin gobara ta hanyar amfani da ƙonannun bululluka domin kare kayayyaki daga tashin gobarar.