Jami’an sojin Operation Forest Sanity haɗin gwiwar da jami’ai na musamman daga Hedkwatar tsaro ta ƙasa sun hallaka ‘yan bindiga da shida tare da Kwato makamai a Jihar Kaduna.

Jami’an Sun samu nasarar ne a yayin wani samame da suka kai maboyar ‘yan bindigan da ke Jihar.
Daraktan yaɗa labaran rundunar Sojin Manjo Janar Musa Danmadami ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya sanyawa hannun yana mai cewa sojin sun lalata sansanonin ‘yan ta’addan.

Dan Madami ya kara da cewa A ranar Jumu’a Jami’an rundunar haɗin gwiwar da sauran jami’an hedkwatar tsaro na musamman ne suka kaddamar da harin a maɓoyar ‘yan bindiga da ke kauyen Maidaro a yankin Giwa ta Jihar.

Kazalika ya ce a yayin harin jami’an da yan ta’addan sun yi musayar wuta a har ta kai ga sun hallaka shida Shannan su ka kwato bindiga kirar AK-47 guda 5 da kuma alburusai na musamman guda 192.
Sannan sun sake kwato wasu alburusai guda 74 da bindigun AK-47 Magazines guda 47 da kuma abubuwan fashewa 3 Radio uku PKM ɗaya da kuma babura uku.
Dan Madamin ya ce rundunar soji ta jinjina tare da yaba wa jami’an rundunar Operation Forest Sanity bisa nasara .
Sannan ta yi kira ga al’umma da su riƙa taimakawa jami’an sojin da bayanan sirri kan ayyukan ‘yan ta’adda da sauran miyagu masu aikata muggan laifuka a yankunansu.