An zaɓi sanata Godswill Akpabio a matsayin a matsayin sabon shugaban majalisar dattawa ta ƙasa.

Sabon shugaban ya kayar da abokin takararsa Abdulaziz Yari na jihar Zamfara.
Bayan zaɓen sa a matsayin shugaban majalisa ta 10, an rantsar da su a matsayin sabbin wakilai.

Saanata Barau Jibril shi ya zama mataimakin shugaban majalisa ta 10.

Godwills Akpabio da mataimakinsa Barau Jibril sun fito daga jam’iyya mai mulki ta APC.
Wasu daga cikin masu neman kujerar sun janyewa Godwills Akpabio da mataimakinsa kafin ranar rantsarwa.
An ssha dambarwa tun kafin da shugaban kasaa Bola Ahmed Tinubu ya ayyana mutanen a matsayin waɗanda ya ke goyon baya.