Gwamnan jihar Ondo Rotimi Akeredelu ya miƙa ragamar mulkin jihar ga mataimakinsa yayin da yayi tafiya domin duba lafiyarsa.

Gwamnan ya damka mulkin jihar a hannun mataimakinsa Lucky Aiyedatiwa.
Aa waata wasika da majalisar dokokin jihar ta karba wadda gwamnan ya aike mata, ya ce zai shafe kwanaki 21 a kasar waje domin duba lafiyarsa.

Shugaban majlaisar wanda ya karanta takardar ya ce gwamnan zai koma bakin aiki a ranar 6 ga watan Yuli na shekarar da mu ke ciki.

Gwamnan ya bai wa mataimakinsa cikakken iko domin jan ragamar mulkin jihar.
A baya, jam”iyyar Adawa a jihar ta buƙaci gwamnan ya mika ragamar mulkin jihar ga mataimakinsa sanadin rashin lafiyar da yake fama da ita.