Wata kotun masana’antu a Najeriya da ke zamanta a Abuja ta bayar da umarnin kama sufeton ƴan sanda na kasa Usman Alkali Baba da sakataren hukumar.

Umarnin ya biyo bayan kin bin umarnin kotu da su ka yi wanda kotun ta ce hakan rashin daa ne.

Tun a baya kotun ta bayar da umarni ga sufeton a kan tilastawa wasu jami’ai ritaya bayan kammala wasu horo a makarantar hosar da yan sanda.

Jami’an sun kai korafi a kan yaadda sufeton ya tilasta musu barin aiki kamar yadda alkalin kotun Justice Oyewuni Oyebuola.

Kotun ta bayar da umarni ga sufeton da kuma sakataren hukumar yan sanda da hukumar aikin dan sanda domin mayar da jami’an bakin aiki.

Bayan umarnin kama sufeton Yan sandan kotun ta dage sauraron karar zuwa ranar 9 ga watan Oktoban shekarar da mu ke ciki.

Leave a Reply

%d bloggers like this: