Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya sanya hannu a kan dokar da za ta bai wa ɗalibai damar yin karatu bashi.

Shugaban ya sanya hannu a ranar Litinin yayin da ake tsaka da murnar zagayowar ranar demokradiyyar a Najeriya.

Bayar da bashin tallafin karatu naa daga cikin manufofin da shugaban ya bayyanawa ƴan ƙasar yayin yaƙin neman zabensa.

Tsohon shugabna majalisar wakilai ta tarayya Femi Gbajabiala ne ya gabatar da kudirin wanda majalisar ta amince da shi a shekarar 2022 da ta gabata.

Dokar za ta bayar da damar kafa bankin domin bai wa dalibai rance masu son yin karatu a kwaleji ko jami’a ko makarantar koyon sana’ar hannu.

Haka kuma za’a a bayar da talafin bayan an bai wa dalibi gurbin karatu.

Haka kuma dokar ta ce za dalibi ba zai fara biya ba har sai ya kammala karatunsa da kuma hidimaar kasa sannan ya samu aiki sai a fara cire kashi 10 cikin 100 na albashinsa.

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: