Gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello ya sanar da korar kwamishinan noma, Mista David Apeh.

Gwamnan ya kori kwamishinan ne a ranar Talata.

Haka nan kuma ya kori mataimaki na musamman kan harkokin agajin gaggawa, Mista Danladi Isah-Yunusa, da Hajiya Maryam Salifu, shugabar hukumar kula da otel da harkokin yawon buɗe ido ta jihar Kogi.

Korar mutanen uku dai na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da sakatariyar gwamnatin jihar, Misis Folashade Ayoade-Arike, ta fitar a Lokoja.

Duk da cewa ba a bayar da dalilin korar Apeh ba, Ayoade-Arike ta ce gwamnan ya amince da dakatar da kwamishinan nan take.

Sai dai ta ce an sallami Isah-Yunusa da Maryam Salifu daga muƙamansu ne saboda dalilai na karya ƙa’idojin aiki.

Hakan dai na zuwa ne a ƙasa da watanni shida da suka rage a gudanar da zaɓen  a jihar Kogi.

 

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: