Wata Kungiya mai zaman kanta a Jihar Kano ta bukaci a gurfanar da ɗan majalisa mai wakiltar Tudun Wada da Doguwa a gaban kotu.

Ƙungiyar ta bukaci a gurfanar da Alasan Ado Doguwa a gaban kotu kan zargin kisan kai da mallakar bindigu ba bisa ka’ida ba.

Hakan na kunshe ne a cikin wata wasika mai dauke da sa hannun Babban Daraktan kungiyar Comr. Umar Ibrahim Umar.

Sannan ya kuma aikawa babban lauya kuma kwamishinan shari’a na jihar Kano a yau Laraba.

A cikin wasikar, Comr. Umar ya ci gaba da cewa, “Wannan bukata ta biyo bayan sanarwar da tsohon lauya kuma kwamishinan shari’a M.A Lawan ya yi na rashin gurfanar da Doguwa a gaban kuliya bisa dalilin da ya sa aka nemi a sake duba kundin shari’ar don sanin wanne irin mataki ya kamata a dauka.

A baya jami’an yan sanda sun gurfanar da Doguwa a kotu bayan gudanar da bincike a kan zargin da ake masa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: