Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara  Zulum, ya raba motocin noma 442 da injinan noma da garmuna guda 312 da kuma takin zamani nau’in MPK ga manoma a jihar.

Gwamnan ya bada umarnin bai wa kowacce daga kananan hukumomin jihar 27 taraktoci 5, da kuma guda daya ga kowacce daga 312 na jihar domin sayar wa manoma a kan rabin farashin da gwamnati ta sayi motocin.

Ya bayyana cewa za a sayar wa manoma taraktocin ne ta hannun kungiyoyin hadin gwiwar manoma.

Da yake jawabi yayin kaddamar da motocin na noma a Maiduguri, Zulum ya ce,  gwamnatin sa ta sayi kayayyakin noman ne domin sayar wa  manoma bisa rangwame a fadin jihar.

Ya kuma ba da umarnin kafa kwamitin sayar da kayayyakin noman a kowacce karamar hukuma, inda kwamitin zai kunshi babban sakataren ma’aikatar noma da albarkatun kasa, babban sakataren hukumar raya ayyukan noma ta jihar, shugabannin jam’iyyar APC mai mulki a kananan hukumomi da  kwamitin mika mulki na kananan hukumomin.

Sauran sun haɗa da ’yan majalisar dokokin jihar Borno, shugabannin ayyukan gona na kananan hukumomin da sauran su a kowace karamar hukumar.

Zulum ya koka kan yadda wasu miyagun da gwamnati ta saya don a rabawa manoma, inda ya ce duk wanda aka samu yana aikata hakan nan gaba za a yi maganin sa yadda, babu sani, babu sabo.

Gwamnan ya kuma tabbatar da cewa gwamnatin sa a shirye take ta yi wa kowa hidima ba tare da la’akari da matsayinsa a cikin al’umma ba.

Ya kuma yi alkawarin kara samar da karin kayayyakin aikin noma da takin zamani da irin shuka ga manoma domin rarrabawa a fadin jihar da zimmar bunkasa noman rani.

Leave a Reply

%d bloggers like this: