Shugaban Najeriya Bola Ahmad Tinubu ya dakatar da shugaban hukumar yaki da masu yiwa tattalin arzikin Kasa Zagon Kasa ta EFCC Abdul Rashid Bawa.

Hakan na kunshe ta cikin wata sanarwa da daraktan yada labaran Ofishin Sakataren gwamnatin tarayya ya fitar a ranar Laraba.
Shugaba Tinubu GCFR ya amince da dakatar da Abdulrashid Bawa CON daga matsayinsa na shugaban hukumar ta EFCC ne domin gudanar da bincike akan ayyukansa a yayin da yake ofishinsa.

Sannan an Bukaci da Bawa da ya gaggauta mika harkokin ofishinsa ga daraktan ayyuka a hukumar domin ci gaba da jagoranci harkokin ofishin shugaban hukumar har zuwa lokacin da za a kammala bincike.

Dakatar war na zuwa ne bayan wasu manyan zarge-zargen cin zarafin ofishinsa da ake yi masa.
Bayan dakatar da shugaban hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arzikin ƙasa zagon ƙasa ta EFCC jami’an tsaron DSS sun gayyaceshi domin amsa tambayoyi.