Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya tafi ƙasar Faransa don halartar taron harkokin kudi na duniya.

Za a yi taron a ranar Alhamis a birnin Paris don yin nazari a kan hada-hadar kudi tare da sanya hannu a sabuwar yarjejeniyar.
Hakan na kunshe a wata sanarwa da mai bai wa shugaban ƙasar shawara a kan ayyuka na musamman Dele Alake ya sanyawa hannu a yau.

Taron zai duba hanyoyin da za a tallafi kasashen da su ke wani hali.

Haka kuma shugaban da wasu shugabannin kasashe za su yi duba a kan yadda za a farfaɗo da tattalin arziki da aka faɗa a lokacin annobar Korona.
A na sa ran shugaban zaai dawo Najeriya a ranar Asabar 24 ga watan da mu ke ciki.
Wannana ce tafiya ta farko da shugaban zai yi a matsayinsa na shugaban Najeriya.