Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya bayar da umarnin rushe dukkan shugabannin majalisun da ke kula da ayyukan ma’aikatun gwamnatin tarayya.

Tashar talabijin ta kasa ta rawaito cewa umarnin shugaban ya shafi ma’aikatu, cibiyoyi, hukumomi da wani kamfanin gwamnatin tarayya da ke Najeriya.

Hakan na zuwa ne jim kadan bayan da Tinubu ya sallami wasu hafsoshin tsaro da kwastam.

Sallamr na zuwa ne a ranar Litinin ta bakin Darektan yada labaran Ofishin sakatare gwmati Tarayya Willie Bassey.

Dakatar da shugabannin da aka yi bai shafin wasu ma’aikatu da hukumomin da ba sa cikin karkashin sashe na 153 (i) na kundin tsarin mulkin kasa na 1999 ba.

Sanarwar ta bayyana cewa wadanda abin ya shafa su gaggauta barin ofisoshinsu ba tare da bata lokaci ba.

Jaridar Punch ta rawaito daga cikin wadanda aka kora babu hukumomin INEC, FCC, CCB, RMFAC da PSC.

Sanarwar ta kuma umarci hukumomin su kai maganar zuwa ma’aikatunsu,domin wadanda su ke a matsayin Minitoci a yanzu za su dauki mataki a madadin majalisar.

Bassey ya kara da cewa hukumomin za su aika takardunsu ta karkashin manyan Sakatarori,sannan Sakatarori za su gabatar da bukatun hukumomin cibiyoyi, ma’aikatu ko kamfanonin zuwa ga shugaban kasa ta ofishin sakataren gwamnatin kasa.

Ta ce wannan umarni ya fara aiki tun daga Juma’a da ta gabata.

Sannan an kuma umarci ma’aikatan gwamnati su yi cikakkiyar biyayya kamar yadda ake bukata..

Leave a Reply

%d bloggers like this: