Shugaba Kasa Bola Tinubu ya karawa Nuhu Ribado girma daga Mashawarci Na Musamman Kan Tsaro zuwa Mai Bada Shawara Kan Tsaron Kasa.

shugaban ya kara masa matsayin ne a ranar Litinin, a matsayin Mai Bada Shawara Kan Tsaron Kasa.
Shugaban ya nada Ribado ne tare da nadin sabbin hafsoshin tsaro ciki har da shugaban hafsan sojojin kasa da na tsaro.

Shugaban ya bayyana cewa nadin zai fara aiki ne nan take.

A ranar Alhamis din da ta gabata ne Shugaban kasar ya sanar da nadin Ribado a matsayin mashawarci na musamman kan tsaro tare da wasu mashawarta bakwai.