Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya amince da mayar da wasu hukumomi biyu na ƙasar karkashin kulawar mataimakinsa.

Shugaba Tinubu ya yarda da mayar da hukumar bayar da agajin gaggawa ta ƙasa NEMA da hukumar aikin hajji ta kasar NAHCON ƙarƙashin ofishin mataimkainsa Sanata Kashim Shettima.

Hakan na kunshe a wata sanarwa da daraktan yaɗa labaran ofishin mataaimakin shugaban kasar Olusola Abiola ya sanyawa hannu.

Sanarwar da aka fitar a ranar Talata, ta nuna amincewar komawar hukumomin la’akari da yadda aka kafa su.
An cire hukumomin biyu daga ofishin mataimkain shugaban kasa a lokacin tsohon shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.
A baya an mayar da hukumar NEMA karkashin kulawar ma’aikatar jin kai ta kasa, sai hukumar aikin hajji NAHCON da aka mayar da ita karkashin kulawar ma’aikatar harkokin kasashen waje.