Yayin da ake gab da karewar wa’adin tsagaita wuta a kasar Sudan wani kazamin fada ya sake barkewa a birnin kasar.

Rahotanni sun ce an gwabza faɗa a dukkan sassan birnin Khartoum.

Akwai wa’adin tsagaita wuta a tsakanin dakarun sojin biyu wanda zai kare a yau Laraba.

Sai dai kafin karewar wa’adin wani kazamin faɗa ya sake barkewa a babban birnin kasar.
Kasashen Amuruka da Saudiyya sun ahiga tsakani domin ganin an tsagaita wuta a baya bayan nan, wanda ake zargi dakarun sun karya yarjejeniyar da aka cimma matsaya a kai.
Tun a watan Afrilu aka fara samun sabani tsakanin dakarun sojin kasar wanda hakan y
ayi silar asarar dumbin dukiya tare da lalata kayan gwamnati.