Jami’an yan sanda a jihar Imo sun kama mutane biyar da ake zargi yan fashi da makami ne.

Mutane biyar da aka kama dukkaninsu yan kasa da shekara 30 a duniya.

Mai magana da yawun yan sandan jihar Henry Okoye ya ce jami’an su sun kama mutanen a maboyarsu da ke Ama Hausa da ke Owerri ta arewa a jihar.

Sannan sun kwato bindigu kirar pistol guda biyu daga wajensu.
Sannan jami’an na ci gaba da kokarin kamo wasu da ake zargi sun tsere.
Haka kuma wadanda aka kama za su tabbata sun gurfanar da su a gaban kotu bayan sun kammala bincike.
Kwamishinan yan sandan a jihar ya tabbatar da cewa zai yi iya kokarinsa don ganin an kawar da masu garkuwa da mutane da sauran ayyukan ta’addanci a jihar