Ma’aikatar ilimi na jihar Kano ta amince da Juma’a, 23 ga watan Yuni, a matsayin ranar fara hutun bikin babban sallah ga dukkanin makarantun jeka ka dawo da na kwana a jihar.

 

Bikin babbar sallah wanda zai shafe tsawon mako guda zai kare a ranar Asabar, 1 ga watan Yuni.

 

Sakataren din-din-din na ma’aikatar ilimi na jihar, Malam Ahmad Tijjani Abdullahi, ya bukaci iyaye da su tabbatar da komawar yaransu makaranta a ranakun da aka sa za a dawo.

 

A cewar wata sanarwa dauke da sa hannun daraktan labarai da wayar da kan jama’a na ma’aikatar ilimi a jihar Kano Alhaji Aliyu Yusuf, da aka gabatar ga manema labarai a Kano a ranar Alhamis, gwamnatin jihar ta yi kira ga iyaye a jihar da su kwashe yaransu zuwa gida a safiyar Juma’a.

 

Malam Abdullahi ya kuma bukaci iyaye da su tabbatar da bayar da hadin kai kan ranakun da aka amince dalibai za su dawo.

 

Ya kuma yi masu barka da bakukuwan sallah da za yi sannan ya roke su da su zamo masu amfani ga iyayensu da kuma guje ma yawo mara amfani a lokacin hutun sallah.

Leave a Reply

%d bloggers like this: