Sabon shugaban hukumar korafe-korafe da yaki da cin hanci da rashawa ta Jihar Kano, Barista Muhuyi Magajin Rimin-Gado, ya yi alkawarin sake bude binciken da ake yi wa tsohon Gwamna Abdullahi Umar Ganduje kan faifan bidiyon da janyo cece-kuce.

 

Jaridar Daily Nigerian, ta yanar gizo, ta fitar da wasu faifan bidiyo na Ganduje da ake zargin yana karbar kudade daga hannun ‘yan kwangila.

 

Tsohon Gwamnan ya musanta zargin, yana mai cewa faifan bidiyon an yi masa cushe.

 

Sai dai da yake magana a gidan talabijin na Trust TV, Rimin-Gado, wanda Ganduje ya tsige bayan wata hatsaniya, amma Gwamna Abba Kabir Yusuf ya mayar da shi bakin aiki, ya ce binciken ya zama dole.

 

Rimin-Gado da yake martani kan abin da ya fada game da bidiyon dala a wata hira da aka yi da shi a baya, ya ce, yana nufin duk maganar da ya fadi lokacin da yake kan mulki, sun bude bincike amma akwai wasu iyakoki a lokacin domin shi ne gwamna mai ci.

 

Ya kuma yi magana kan batutuwa da dama, inda ya musanta cewa an yi amfani da shi wajen tsige Alhaji Muhammadu Sanusi daga matsayin sarkin Kano a wancan lokaci.

Leave a Reply

%d bloggers like this: