Hukumar kula da bashi ta Najeriya DMO ta gargadi gwamnatin tarayya akan karin karbo bashin kudi a wannan lokaci.

Jaridar Vanguard ta rawaito cewa hukumar ta bukaci da shugaban Kasa Bola Tinubu da ya guji karbo wa Kasar Bashi.

Hukumar ta kara da cewa ba ta goyon bayan kara karbo bashi ganin cewa kashi 73.5 na kudin shigar da Kasar za ta samu a shekarar nan duk zai tafi ne a wajen biyan bashin da aka karbowa kasar.

DMO ta bayyana cewa kason kudin shigar da ke tafiya a wajen biyan tsofaffin basukan ya yi yawan da bai dace a sake karbo wani bashin kudi ba.

Hukumar ta kuma bukaci gwamnatin tarayya da ta nemi hanyoyin da za tabi wajen ganin ta kara samun kudin shiga a cikin lalitar Najeriya.

DMO ta kara da cewa gwamnatin tarayya ta iya karbo bashin hankali, inda ta ce wajibi ne harajin da za a samu a kasafin kudin shekarar da muke ciki ya karu.

Hukumar ta bayyana cewa a hasashen da aka gudanar za a iya samun kudin shiga Naira Tiriliyan 10.49, inda ta ce sai gwamnati ta samu abin da ya kai Naira Tiriliyan 15.5 sannan a iya karo bashi.

Jaridar Punch ta bayyana cewa bashin da ake bin Najeriya ya doshi naira tiriliyan 81.

Wanda hakan ya tilasta hukumar ta DMO jan hankalin gwamnatin da shugaba Tinubu kan gujewa sake karbowa kasar bashi.

Leave a Reply

%d bloggers like this: