Gwamnan Jihar Sokoto Ahmad Aliyu ya bayar da umarnin gaggauta biyan ma’aikatan Jihar albashin watan Yuni da muke ciki.

Umarnin na zuwa ne a ranar Alhamis ta hannun Sakataren yaɗa labaran gwamnan Abubakar Bawa cikin wata takarda da ya sanyawa hannu.
Daga cikin wadanda za a bai’wa albashin ciki harda dukkannin ‘yan fanshon da ke Jihar.

Sanarwar ta bayyana cewa gwamnatin Jihar ta yi hakan ne domin bai wa ma’aikatan Jihar da ‘yan fanshon damar gudanar da bukukuwan Sallah babba cikin walwala da jindadi.

Gwamna ya kuma tabbatarwa da ma’aikatan Jihar aniyar gwamnatinsa na farfaɗo da martabar ma’aikatan ta hanyar tabbatar da jin daɗi su da walwalarsu a kowanne lokaci.
Gwamnan ya bukaci ma’aikatan da su kiyaye lokaci gaskiya da kuma sadaukarwa a wajen ayyukansu.
Kazalika yayi kira ga ɗukkan mutanen Jihar da su ci gaba da yi wa gwamnatin Jihar addu’a domin ganin ta samu nasarar biyan bukatunsu da ta daukar musu alƙawari.