Jam’iyyar PDP reshen jihar Benue ta mayarwa da gwamna Jihar martani akan matakin da ya ɗauka na dakatar da shugabannin kananan hukumom 23 a Jihar.

Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa majalisar dokokin Jihar ce ta dakatar da shugabanin kananan hukumomin domin bayar da isasshiyar damar gudanar da bincike akan zargin sama da fadi da wasu kuɗaɗe.

Mai magana da yawun jam’yyar ta PDP, Bemgba Iortyom ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya fitar, ya ce gwamna Alia da majalisar karkashin jagorancin APC duk sun shiga cikin ruɗani.

Kakakin ya ce gwamna Jihar wanda ya aike da sakon dakatar da shugabannin kananan hukumomi ga majalisar ta hannun shugaban ma’aikatansa,ya fake da sunan gudanar da bincike akan kuɗin shiga da waɗanda suka fita daga asusun kananan hukumomi daga watan Fabrairu zuwa Afrilu 2023 ya nemi majalisa ta yi bincike kuma ta bada shawarar da ta dace.

Bayan aikewa da majilsar takardar dakatarwar majalisa ta kafa wani kwamitin mai dauke da mutum uku wadanda za su gudanar da bincike kuma su kawo mata bayanai cikin mako biyu.

Kakakin na PDP ya ce matakin hakan ya saba wa umarnin Kotu, bayan haramta wa gwamnatin Jihar dakatar da zababbun shugabanni a matakin kananan hukumomi.

Sannan ya ce gwamnatin ba ta san komai ba ballantana ta daukaƙa kara akan hukuncin da Kotun ta yanke.

Leave a Reply

%d bloggers like this: