Majalisar dokokin Jihar Filato ta amincewa gwamnan Jihar da ya karbo bashin naira biliyan 15.

Majailsar ta amincewa gwamnan ne a yayin zaman Majalisar da ya gudana a ranar Alhamis.
Wasikar neman amincewar da gwamnan ya aikewa da majalisar na nuni da cewa kudin bashin da zai karbo zai yi amfani da su ne wajen biyan albashin ma’aikata da kuma siyo kayan noma a Jihar.

A yayin zaman Majalisar Kakakin majalisar Honorabul Matthew Sule ne ya karanto wasikar da gwamnan ya aike ga sauran mambobin majalisar domin su amince masa da ya karɓo bashin.

Gwamnan yayi bayanin cewa ma’aikata a Jihar na bin gwamnati bashin albashi da ya kai naira biliyan 11.