Hukumar tsaron farin kaya ta DSS ta bayyana cewa ta gano wasu shirye-shiryen wasu batagari na kai hare-hare a wasu guraren bauta da filayen wasanni da wasu guraren a lokacin bukukuwan babbar sallah.

Mai magana da yawun hukumar Peter Afunanya shine ya tabbatar da hakan, inda yayi kira ga masu manyan shaguna da su kara sanya idanu a wannan lokacin da muke ciki.
Afunanya ya ce jami’an tsaron DSS da na ‘yan sanda da jami’an soji ne su ka samu nasarar gano shirin tare da gano wasu makaman IED masu tashi.

Afunanya ya yi kira ga jama’a da su yi gaggawar sanar da jami’an tsaro da zarar sun hadu da mutanen ba su yadda da su ba.

Hukumar ta kuma bukaci mutane su sanya idanu a yankunan su kafin bukukuwan sallah, bayan shirin da jami’an su ka gano cewa ‘yan ta’addan na shirin kai hari a dakunan bauta da guraren shakatawa kafin sallar da Kuma bayan sallar.
Afunanya ya yi kira ga shugabanni da masu kula da guraren taro kasuwanni shaguna da sauran gurare da su sanya idanu tare da sanar da jami’an dukkan wani motsi da ba su yadda dashi ba.
Hukumar ta ce za ta hada hannu da sauran jami’an tsaro da ke Najeriya domin ganin an dakile yunkurin ‘yan ta’addan.