sohon Gwamnan Jihar Zamfara Muhammad Bello Matawalle ya raba Naira miliyan 200 ga ‘yan jam’iyyarsa ta APC domin gudanar da shagulgulan bikin babbar sallah.

Shugaban jam’iyyar ta APC a Jihar Tukur Danfulani ne ya tabbatar da hakan a yayin wani jawabi da ya fitar a ranar Lahadi.

Tukur ya kara da cewa Matawalle ya rabawa ‘yan jam’iyyar kudin ne domin samun gudanar da hidimar sallah.

Shugaban ya ce daga cikin wadanda su ka ci gajiyar sun hada da mata, matasa, Marayu, malaman addini, da masu tallata APC da kuma sauran magoya bayan jam’iyyar.

Dan Fulani ya bayyana cewa an kafa Kwamiti na musamman domin ya fara aikin rabawa mutanen kudin domin gudanar da bikin sallah cikin walwala da jin dadi.

Daga bisani Tukur ya godewa Matawalle sakamakon kyautar kudin a lokacin da aka fi bukatartarsa.

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: