Tsohon shugaban kasan Najeriya Muhammadu Buhari ya bayyana cewa aiki mafi wahala a rayuwarsa shi ne shugabantar Najeriya.

Buhari ya bayyana haka ne a yau Laraba wajen sakon barka da Sallah ga yan kasa Najeriya ta bakin Malam Garba Shehu.

Buhari ya ce jagorantar kasa Najeriya shi ne aiki mai wahala da ya taba yi a rayuwarsa.

Sannan ya ce yan Najeriya su jira nasararsa a wurin Bola Ahmad Tinubu.

Sannan ya ce yana mai rokon yan kasar su baiwa sabon shugaban kasa goyan baya.

Tare da cewa goyan bayansu shi ne abun da zai sanya akai kasar tudun mun tsira.

Daga karshe Buhari ya ce yana yiwa musulman kasa Najeriya fatan barka da Sallah tare da maniyyatan da suke aikin hajji da kuma dawowa da su gida Najeriya lafiya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: