Shugaban rukunin masana’antu na Dangote, Alhaji Aliko Dangote, ya ci gaba da rike kundin attajirin da ya fi kowa kudi a Afrika, duk da faduwar darajar Naira a kan dala da ta durkusar da mafi yawan hannayen jari a Najeriya.

A cewar Bloomberg, Dangote ya na da adadin kudade har dala biliyan 15.6 kuma shi ne attajirin da ya fi kowa kudi a Afrika.
Aliko Dangote ne kadai dan Najeriya a cikin jerin sunayen mutane 500 da suka fi kowa arziki a duniya, kuma ya kasance mutumin da ya fi kowa kudi a Afrika na tsawon shekaru 12 da suka gabata.

Babban abokin kasuwancinsa a Najeriya, Abdul Samad Isiyaka Rabiu, ya fice daga jerin sunayen bayan da ya yi asarar kimanin dala biliyan 2.8, sakamakon faduwar darajar Naira.

Rukunin masana’antu na Dangote, shi ke da mallakin babban kamfanin samar da siminti a Afrika, wato Dangote Cement, wanda nan ne babbar hanyar samun kudaden attajirin.
Har ila yau, kamfanin yana samar da sukari, gishiri, taki, da kayan abinci.
A kwanakin baya ne Dangote ya kaddamar da katafariyar matatar mai ta dala biliyan 19, wacce ita ce mafi girma a Afrika.
Sauran ‘yan Afrika da ke cikin jerin masu kudi 500 sun hada da Johann Ruppert, wanda ya hau kan Dangote a jerin attajiran Forbes a matsayin wanda ya fi kowa kudi a Afrika da dukiyar da ta kai dala biliyan 13.3.
Nicky Oppenheimer dan kasar Afrika ta Kudu, Nassef Onsi Sawiris na kasar Masar, Natie Kirsh na Afrika ta Kudu da kuma Naguib Onsi Sawiris na kasar Masar na cikin jerin masu kudin na Bloomberg.
A ranar Laraba, 28 ga watan Yuni, 2023, Dangote ya hau daga na 122 zuwa 111 a jerin masu kudin, bayan samun kusan dala miliyan 20.7 a cikin sa’o’i 24.