Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya yi kira ga alhazan Nijeriya da suka je aikin hajjin bana a kasar Saudiyya da su kwantar da hankalinsu, yana mai cewa abu mai muhimmaci a aikin Hajji shi ne hakuri da sadaukarwa a cikin wahalhalu.

Jakadan Nijeriya a kasar Saudiyya, Ambasada Yahaya Lawal, ne ya isar da sakon shugaban ga alhazan Nijeriya yayin ziyarar da ya kai wa mahajjatan a Mina a ranar Alhamis.

Wakilin Nijeriya wanda ya samu rakiyar takwaransa na kasar Sudan, Ambasada Safiu Olaniyan, shugaban hukumar alhazai ta Nijeriya (NAHCON), Alhaji Zikrullah Kunle Hassan, da kwamishinoninsa da manyan jami’an hukumar NAHCON, ya bukaci alhazan Nijeriya da su ci gaba da gudanar da aikin hajjinsu na bana cikin tsari da zama jakadu nagari na kasarsu a lokacin da suke kasa mai tsarki.

Shugaba Tinubu ya kuma shawarci mahajjatan da cewa, maimakon yin gunaguni game da kalubalen da suke fuskanta, ya kamata su mai da hankali kan muhimmancin tafiya kasa mai tsarki tare da mayar da hankali wajen yi wa Nijeriya addu’a, yana mai cewa kasar na bukatar addu’o’insu don shawo kan kalubalenta.

Yanzu haka an sanar da shugaban kasar kan irin kyawawan dabi’un da suka nuna kuma yana fatan su ci gaba da wakiltar Nijeriya a kasar.

Sannan ya buƙaci su sanya Nijeriya cikin addu’o’insu, domin sun san kalubalen da kasarmu ke fuskanta kuma yana da muhimmanci su yi amfani da wannan dama ta musamman wajen yin addu’a ta musamman don ci gaban Nijeriya, zaman lafiya, kwanciyar hankali da walwala ga ‘Yan ƙasar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: