Hukumar zaɓe mai zaman kanta (INEC) ta bayyana cewa nan ba da jimawa ba zata ɗauki mataki kan dakataccen kwamishinan zaɓen Adamawa, Hudu Ari.

Kwamishinan yaɗa labarai da ilimantar da masu kaɗa kuri’a na INEC ta ƙasa, Festus Okoye ne ya faɗi haka yayin hira a shirin siyasa a yau Juma’a.

Idan zaku iya tunawa, Hudu Ari ya haddasa ruɗani da cece-kuce lokacin da ya ayyana sakamakon cikon zaɓen gwamnan Adamawa tun kafin a gama tattara sakamako.

Ya ayyana Sanata Aishatu Binani ta jam’iyyar APC a matsayin wacce ta lashe zaben a wancan lokacin.

Bayan faruwar haka, shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, ya umarci a gudanar da bincike mai zurfi kan jami’an tsaron da ke da hannu a lamarin wanda ya saɓa wa doka.

Okeyeye ya ce game da batun kwamishinan zaɓen Adamawa (REC) kan san cewa shugaba Buhari ya dakatar da shi tun kafin sauka daga mulki kuma ‘yan sanda sun gayyace shi domin ya yi bayanin abinda ya faru.

Ya kara da cewa sun samu labarin hukumar ‘yan sanda ta gama bincike kuma nan da makonni kalilan zasu sanar da ‘yan Najeriya abinda ya faru.

Leave a Reply

%d bloggers like this: