Tsohon gwamnan Jihar Kano Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya musanta jita-jitar da ake yadawa cewa shine yake juya mulkin kano a yanzu sabanin Gwamnan Jihar Abba Kabir Yusuf.

Kwankwaso ya bayyana haka ne yayin hira da jaridar RFI Hausa a ranar Lahadi.

Kwankwaso ya ce kawai ‘yan adawa ne suke yi masa kazafi, ya ce
a halin yanzu mutane aiki kawai su ke bukata.

Sanata kwankwaso ya ce shi bashi da hannu akan dukkan dukkan ayyukan da gwamnan Jihar Abba Kabir Yusuf ya ke gudanarwa.

A yayin da yake jawabi kan batun rushe wasu gine-gine da gwamnatin ta Kano ke yi ya ce gwamnatin gyara ne ba wani abun tashin hankali ba.

Kwankwaso yace koda a lokacin da yake mulkin kano, sai da mutane suka dinga rokonsa akan ya rushe gidajen su domin a biyasu diyya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: