Gwamnatin tarayyar Najeriya ta yi watsi da rahoton karshe na tawagar sanya idanu a zabukan shekarar 2023 na kungiyar Tarayyar Turai EU akan abubuwan da suka gani a yayin zaben 2023 da aka gudanar.

Mashawarci na musamman ga shugaban kasa Tinubu kan ayyuka na musamman da sadarwa Dele Alake ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi.

Gwamnatin ta ce rahoton da tawagar ta EU ta yi,ta yi ne matsayin aikin zaman tebur da ta yishi a zaune kuma mara kyau.

Gwamnatin ta kara da cewa tawagar ta EU ta tattara takaitaccen bayanai akan zaben, sannan kungiyar ta kuma dogara ne da rade-radin sharhin kafafen sada zumunta da na jam’iyyun adawa da suke yi.

Sanarwar da Aleke ya fitar ta ce rahoton kungiyar ta EU kan zabukan ba zai yi wani tasiri ba kuma kasar ta riga da ta gamsu da sahihancin shugabancin Bola Tinubu.

Daga karshe kuma gwamnatin ta bukaci kungiyoyin da kasashen ketare da su kasance masu adalci gurin tafiyar da nazari ga abubuwan da ke faruwa a Najeriya.

Idan ba a manta ba dai a baya kungiyar ta EU ta ce akwai kura-kurai a zabukan da aka gudanar a Najeriya a ranar 28 ga watan Fabraru da kuma ranar 18 ga watan Maris din shekarar da muke ciki.

Leave a Reply

%d bloggers like this: