Sama da jami’an sojin Sama da naa ruwa da kuma na kasa 50 ne za ayi wa karin girma a Najeriya sakamakon ritayar da aka yi wa manyan jami’an tsaron kasar.

Wadanda za a yiwa karin girman sun hada da wanda suka kai matsayin Birgediya Janar da Kanal za a karawa matsayin zuwa Manjo Janar da Birgediya Janar.

Sannan za kuma a yi wa jami’an sojin ruwa da sojin sama irin karin matsayin.

Karin girman da za a yiwa jami’an sojin zai bada damar maye gurbin wadanda za su bar aiki.

Majalisar da ke kula da harkar karin matsayin na jami’an soji ba tayi zama ba akan batun, amma rahotanni sun bayyana cewa ‘yan aji na 43 a makarantar NDA suma za su samu karin matsayin.

Kawo yanzu ana ci gaba da tattara sunayen jami’an sojin da za a bai’wa hukumamin domin yi masu karin girman.

Wani bincike ya bayyana cewa kusan duka ‘yan aji na 38 na makarantar NDA sun gabatar da takardun ajiye aiki a hedkwatar tun a karshen makon da ya gabata.

Wata majiya itama ta shaida cewa ban da wasu ‘yan aji na 39 da aka yi wa sauyin guraren aiki ba da dadewa ba suma duk za su bar gidan sojin.

Hukumar da ke tabbatar da karin girma a gidajen jami’an sojojin ruwa sama da kuma kasa ne za su tantance sunayen da aka gabatar, kafin a kara masu matsayi.

Leave a Reply

%d bloggers like this: