Hukumar karɓar ƙorafe-ƙorafe da yaƙi da rashawa ta Jihar Kano ta kama kwamishinan ayyuka a zamanin tsohon Gwamna Kano Dr Abdullah Umar Ganduje, injiniya Wada Suleh sakamakon zarginsa da aikata badaƙalar Naira biliyan daya.

Hukumar ta Kama kwamishinan ne bisa tuhumar biyan kuɗi ga kamfanonin North Stone Construction Company Nigeria Limited, Arfat Multiresources Limited da 1st Step Construction ba bisa ƙa’ida ba.
Wata majiya ta shaidawa Jaridar Daily Trust ce an yi gaggawar sakin kuɗin ne a watan Afrilun da ya gabata na shekarar da muke ciki bayan da jam’iyyar APC ta faɗi a zaɓen gwamnan Jihar ta Kano.

Majiyar ta kara da cewa an fitar da kudadin ne da sunan kwangilar gyaran wasu tituna a Jihar.

A yayin wani bincike da hukumar ta gudanar ya nuna koda ƙasa ba a zubawa Titinun ba.
Kawo yanzu dai hukumar ta fara karɓar shaida daga ma’aikatan gwamnati bisa yadda aka ba su umarnin sakin kuɗin cikin gaggawa.